Monday, 11 November 2013

Jam’iyyar APC ta fara zawarcin gwamnonin PDP guda Bakwai

Shugabannin Jam’iyyar adawa ta APC a Najeriya sun kai ziyara garin Kano da Jahar Jigawa da Sokoto inda suka gana da Gwamnonin Jahohin uku Rabi’u Musa Kwankwaso da Sule Lamido da Aliyu Wamakko domin zawarcinsu, a wani yanayi da kan iya zama baraka ga Jam’iyyar PDP mai mulki. An kwashe sa’o’I shugabannin na APC suna ganawa da gwamnonin Kano da Jigawa bayan sun gana da Gwamnan Sokoto Aliyu Magatakarda Wamakko a Sokoto bayan kammala biki bude Sabuwar Jami'ar Jahar. Shugabannin Jam’iyyar da suka gana da gwamnnonin sun hada da Janar Muhammadu Buhari tsohon shugaban kasa da Tsohon Gwamnan Lagos Bola Ahmad Tinubu da shugaban Jam’iyyar APC Bisi Akande da mataimakinsa Aminu Masari da kuma Nuhu Ribadu tsohon shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC. “APC ta shirya, ta zo ta ga da gwamnoni domin ta yi masu bayani game da tafiyarmu” Inji Buhari a lokacin da ya ke zantawa da Isa Dandago Wakilin RFI Hausa a Kano. Jam’iyyar APC ta samu kafar zawarcin Gwamnonin ne na PDP saboda takun sakar da suke yi tsakaninsu da uwar Jam’iyyarsu mai mulki a Najeriya Gwamnonin Sokoto da Kano da jigawa dukkaninsu gwamnoni da ke adawa da Uwar Jam’iyyar PDP, lamarin da ya sa suka kafa sabuwar PDP tare da jagorancin Alhaji Atiku Abubakar tsohon Mataimakin shugaban kasa. Sauran Gwamnonin da ke adawa da Uwar Jam’iyyarsu ta PDP sun hada da Gwamnan Niger Babangida Aliyu da Gwamnan Adamawa Murtala Nyako da Abdulfatah Ahmad na Kwara da kuma Gwamnan Rivers Rotimi Amaechi wadanda suka nemi a tsige shugaban PDP Bamanga Tukur. Mista Buhari yace sun gana da Wamakko na Sokoto da Kwankwaso na Kano da Lamido na Jigawa kuma sun yada wa gwamnonin manufofinsu. Tuni dai Jam’iyyar ta APC ta nada Gwamnan Lagos a matsayin wanda zai jagoranci tattaunawar zawarcin Gwamnonin na PDP. Sai dai Gwamnan Jigawa Sule Lamido ya kaucewa batun cewa ana neman zawarcinsa, yana mai cewa ya gana da shugabannin Jam’iyyar APC ne domin samar wa ‘Yan Najeriya hanyoyin ci gaba. Yanzu haka wata Majiya tace Shugabannin APC za su nufi zuwa Jahar Adamawa domin ganawa da Murtala Nyako babban mai adawa da jagorancin Bamanga Tukur na PDP.

No comments:

Post a Comment