An kori Ministar sadarwar kasar Ghana, Victoria Hammah bayanda aka dauki muryarta tana cewar za ta ci gaba da siyasa har sai ta mallaki dala miliyan daya.
A muryarta da aka rarraba a Ghana ta ce " idan mutum nada kudi, zai iya juya mutane".
Kawo yanzu Ms Hammah bata maida martani ba a kan wannan sakon ko kuma korarta da aka yi.
Wakilin BBC a Accra ya ce ta taka muhimmiyar rawa wajen sake zaben Shugaba John Mahama a bara.
A watan Agusta, ta ce tana fuskantar matsin lamba a kan ta saci kudin gwamnati saboda mutane sun zaci tana da arziki.
No comments:
Post a Comment