Monday, 18 November 2013

Matsalar Tsaro a Najeriya

A shekarar 2009 ne Kungiyar Jama'atu Ahlil sunnah Lid Da'awati wal Jihad da ake kira Boko Haram ta kaddamar da hare hare domin daukar fansan kisan da aka yi wa Shugabansu Muhammad Yusuf da mambobinsu, kuma tun a lokacin Najeriya ta fada cikin matsalar tsaro bayan gwamnatin Yar'adua ta yi wa tsagerun Niger Delta afuwa. Kungiyoyin kare Hakkin bil'adama sun ce sama da mutane 3,000 ne suka mutu tun fara kaddamar da hare haren kungiyar Boko Haram, tare da zargin Jami'an tsaro da kisan fararen hula da sunan farautar 'yan kungiyar.

APC ta nemi a soke zaben Anambra

Jam'iyyar adawa ta APC a Nigeria ta bukaci hukumar zabe ta kasar, ta soke zaben gwamnan jihar Anambra wanda aka gudanar ranar Asabar da kuma wanda aka karasa ranar Lahadi. Jam'iyyar ta yi zargin cewa kundin rajistar da aka yi amfani da shi a zaben gurbatacce ne. Ta kuma ce a sakamakon haka an hana dubban magoya bayanta kada kuria'a . Jam'iyyar ta APC ta kuma ce ta na da kwakkwarar shaida a kan lamarin. Sai dai hukumar zabe mai zaman kanta ta musanta wannan zargi. Ta kuma ce ba ta da dalilin soke zaben saboda sahihancin kundin rajistar da aka yi amfani da shi.

Za'a sake zabe a wasu sassan Anambra

Hukumar zabe ta kasa a Nigeria ta ce za ta sake gudanar da zaben gwamna a wasu sassa na jihar Anambra saboda matsalolin da aka fuskanta wurin gudanar da zaben. Hukumar dai ta ce kawo yanzu jami'yyar APGA mai mulkin jihar ce kan gaba da kuri'u 174,710, jam'iyyar PDP mai mulkin Nigeria na biye da kuri'u 94,956 yayinda babbar jam'iyyar adawa ta APC ke da kuri'u 92,300. Sai dai hukumar ta ce ba za ta iya baiyana wanda ya yi nasara ba sai bayan kammala ragowar zaben saboda kuri'un da suka rage ba'a kada ba sun dara tazarar da ke tsakanin jam'iyyar da ta zo ta daya da kuma mai bin ta. Hukumar dai ta bayyana sakamakon zaben ne a daidai lokacin da 'yan takarar wasu jam'iyyu da suka hada da APC da Labour da PDP suka yi wani taron manema labarai a jiya, inda suka nuna rashin amincewarsu da zaben. Wasu kungiyoyi masu zaman kansu ma dake sa ido a zaben, sun nuna rashin gamsuwarsu da yadda aka gudanar da shi. Rahotanni sun ce ba'a kai kayan zabe da wuri ba a wasu mazabu, kuma a rajistar masu zaben ma babu sunayen mutane da dama, kazalika ma suka ce akwai wasu wuraren da ba a yi zaben ba.

Bafaranshen da aka kama a Nigeria ya isa gida

Bafaranshen nan da aka sace a Nigeria ya isa gida bayanda ya tsere daga wadanda suka yi garkuwa da shi a wani yanayi da shugaban kasar Faransa Francois Hollande ya ce yayi kama da littattafan labarai.

Thursday, 14 November 2013

An sace shanu sama da 1000 a Pilato

Sakataren kudi na kungiyar Miyatti Allah ta Fulani makiyaya reshen jihar Pilato Malam Salihu Jauro ya ce lamarin ya faru ne a kauyen Sit dake tsakanin Pankshin da Langtan ta arewa. Makiyayan na neman mahukunta da su basu cikakken tsaro tare da dabbobinsu. A mafi yawan lokuta dai satar shanu na haddasa rikicin kabilanci a yankin. Jihar Pilato ta sha fama da rikicin kabilanci da addini tsawon shekaru 14.

Najeriya na neman sulhu da Boko Haram

Gwamnatin Najeriya ta ce abin da ta sa a gaba shi ne kokarin sulhuntawa da 'yan kungiyar da wasu ke kira Boko Haram ba maganar gurfanar da su gaban kuliya ba. Mahukunta a Najeriyar sun ce ba a maganar shari'a sai sulhu ya gagara. Gwamnatin dai na mai da martani ne dangane da matakin da majalisar dinkin duniya ta dauka na sanya 'yan kungiyar Jama'atu Ahlis sunnah lidda'awati wal jihad da wasu ke kira Boko Haram a sahun masu aikata laifukan yaki idan aka tabbatar da aikata laifukan da ake zarginta da yi. Wannan matakin zai ba da kafar gurfanar da duk wani dan kungiyar da ake zargi a kotun hukunta laifukan yaki ta duniya da ke Hague.

Boko Haram: Mutane 40,000 sun gudu Niger

Mutane kusan dubu 40 ne suka tsallaka iyakar Nigeria zuwa Jamhuriyar Niger sakamakon rikicin kungiyar Boko Haram.

Tuesday, 12 November 2013

Me ya sa shugabannin Afrika ke mutuwa a kan mulki?

Abu ne da ba kasafai yake faruwa ba, shugaban kasa ya mutu a yayin da yake jan ragamar mulki. Sai dai tun shekarar 2008 hakan ya yi ta faruwa har sau 13 a fadin duniya.Kuma goma daga cikin shugabannin da suka mutu a kan mulki sun fito ne daga nahiyar Afrika. Me ya sa hakan ya fi yawa a nahiyar ta Afrika? Taron mutane dauke da kendira ne suka baibaye gawar shugaban Habasha Meles Zenawi, a yayin da ake wucewa da gawar ta Adis Ababa, kuma ya mutu ne yana da shekarau 57, bayan doguwar rashin lafiya. A watan Yuli ne kuma dubun dubatar mutanen Ghana suka halarci jana'izar shugaban kasar, John Atta Mills, wanda ya mutum yana da shekaru 68 a duniya. Watanni hudu da suka gabata ne, aka shiga makoki a Malawi don mutanen kasar su sami damar halartar jana'izar shugaba Bingu wa Mutharika, wanda ya mutu sakamakon ciwon zuciya yana da shekaru 78. A watan Janairun shekarar 2012 ne kuma shugaban kasar Guinea Bissau, Malam Bacai Sanha ya mutu a wani asibitin sojoji dake Faransa, bayan doguwar rashin lafiya, yana da shekaru 64. Hakan na nufin shugabannin Afrika hudu ne suka mutu a wannan shekarar kadai. Tunanin 'yan jarida Abin damuwa ne ga mutanen kasashensu, abin bakin ciki ga iyalansu, amma su fa masu aiko da rahotanni me suke gani game da mutuwar ta su? Mai aiko da rahotanni ga shafin internet na Daily Maverick na Afrika ta Kudu, Simon Allison ya bayyana cewa " An yi ta kira na ta waya da daddare cewa ga wani shugaban Afrika ya mutu. Na yi tambaya shin me ya sa shugabannin Afrika ke mutuwa?" Tambayar dai ta sa ya duba tsawon rayuwar shugabannin. Inda ya kara da cewa " Ina duba 'yan shekaru kafin yanzu sai na ga jerin shugabannin da suka mutu suna da yawa."Tun shekarar 2008 shugabannin Afrika goma ne suka mutu a kan mulki. Hakika da gaske ne shugabannin Afrika sun fi mutuwa a kan mulki fiye da kowacce nahiya. A cikin wannan lokaci dai shugabanni uku ne kawai suka mutu a sauran sassan duniya. Kuma su ne shugaban kasar Koriya ta Arewa, Kim Jong Il, shugaban kasar Polland, Lech Kaczynski wanda ya mutu a hatsarin jirgin sama da kuma shugaba David Thomson na Barbados wanda ke da cutar sankara. A bayyane yake cewa shugabannin Afrika sun fi mutuwa a kan karagar mulki saboda tsufa fiye da takwarorinsu na wasu nahiyoyi. Bayanin da Simon ya fi amincewa da shi kenan. Kuma ya yi amannar cewa 'yan Afrika sun fi son dattawa a matsayin shugabannin kasa, saboda al'adar dake tattare da girmama manya a yawancin kasashen nahiyar. Dattijai Hakika shekaru 61 ne matsakaita na shugabanin Afrika da kuma a nahiyar Asiya. A nahiyar Turai kuwa shekaru 55 su ne matsakaita, yayin da a kudancin Amurka, shekarun su ne 59 Sai dai wani abin dubawa a nan shi ne tsawon rayuwar al'umma, wanda nahiyar Afrika ke da mafi karanci a kan nahiyar Turai, yakin Latin Amurka da Asiya. Hakan ya biyo bayan yawaitar wasu cututtuka kamar HIV/Aids da rashin kyakyawan tsarin kula da marasa lafiya wanda ke janyo yawan mace-mace a gurin haihuwa. Sannan talauci a lokacin kuruciya da kuma a farkon rayuwa na tasiri na tsawon lokaci, kamar yadda Dr. Goerge Leeson na jami'ar Oxford ya bayyana. "Shugabannin Afrika kafin a zabe su, sun yi rayuwa cikin wahala a baya, kuma hakan zai shafi tsawon rayuwarsu a lokacin da suke kara girma." In ji Dr. Leeson. " Da zarar sun kama mulki, duk da cewa rayuwarsu ta fi ta mutanen kasa ingantuwa nesa ba kusa ba, wanda hakan ka iya kara musu tsawon kwana fiye da 'yan kasa, sun riga suna tare da wuyar da suka sha a baya kuma zai shafi rayuwarsu a wani lokaci." Kodayake ba dukkan shugabannin Afrika ne suka sha wuya a rayuwar su ta baya ba. Amma akwai wasu dalilan da ya kamata a duba kamar siyasa. Shi shugaban Afrika na son dawwama a kan mulki har sai ya mutu, sai dai ba lallai ba ne hakan ya zama ainihin abin da ke faruwa. "Haka batun yake idan ka yi la'akari da shugabanni kamar Omar Bongo da Conte da kuma Gaddafi" A cewar Simon.Ya kara da cewa "Dukkansu sun yi mulkin kama-karya kuma ba su so barin mulki da kashin kansu ba, amma ba haka batun yake ba ga sauran, misali Meles Zenawi ya dade yana mulki, amma kuma shekarunsa 57 ne kawai, haka ma sauran duk suna wa'adin mulkinsu ne ba su ma yi nisa ba tukuna." Yana da muhimmanci a yi la'akari da cewa an duba wannan batu ne tun daga shekarar 2008, kuma ta iya yiwuwa lissafin mutuwar a wannan lokaci akwai kuskure. Amma koma menene ke faruwa, yawan mutuwar na janyo rashin tabbas. Mutuwa a kan karagar mulki na janyo gibi, wanda hakan na da hatsari. Simon ya yi nuni da cewa " Duba abin da ya faru a Guinea-Bissau, lokacin da Sanha ya mutu, juyin mulki ya biyo baya. Wannan na jefa naiyar Afrika cikin wani hali, tun da a tarihi ba ta iya jure gibi a mulki." Sai dai ya yi imanin cewa akwai kyakkyawar fata. " Mutuwar shugabanni a kasashen Zambia da Malawi da Ghana da kuma Najeriya ya sa an samu cigaba da mulkin farar hula ba tare da tashin hankali ba. Hakan ina ganin wata alama ce da za ta sa kwarin gwiwa na cigaban Afrika."

Monday, 11 November 2013

Tsohon Gwamnan Jihar Gombe, Almundahanu da zargi

wamnan jihar Gombe Alhaji Ibrahim Hassan Dankwambo y ace ya gaya ma hukumar yaki da almundahana da zagon kasa ma tattalin arziki EFCC ta bincike tsohon Gwamna Danjuma Goje saboda wasu makudan kudaden da ya ce ya yi rub da ciki a kansu. Gwamnan ya fadi hakan ne lokacin da ya ke karbar rahoton kwamitin Fensho na Kananan Hukumomi da kuma na gwamnatin jihar. Ya ce shi da kansa ya baiwa tsohon gwamnan wadannan kudaden lokacin ya na Babban Akanta-Janar na Nijeriya. A halin da ake ciki kuma ikirarin da tsohon gwamna Danjuma Goje ya yi kwanan nan a wata hirarsu da wakilinmu inda y ace shi ne uban duk wani dan PDP a jihar Gombe ya janyo martani. Wani mazaunin garin Gombe mai suna Abdulkadir Abab, y ace ai dattijo bai sata amma kuma gashi shi Gojen da ke cewa shi dattijo ne, banda tuhumar da yak e fuskanata a kotu an sake gano cewa akwai wata satar makudan kudade da ya yina Naira biliyan biyar da miliyan dari bakwai. Abdulkadir y ace banda wannan zarge zarge na almundahana da yake fuskanta, tsohon gwamnan ya yi sanadin mutuwar wasu mutane da dama; banda wadanda ya kora ko kuma ya janyo masu ciwuwwuka saboda tozartawa da cin mutunci.

APC na zawarcin Gwamnonin sabuwar PDP

A yau ne ake saran manyan shugabannin jam'iyyar hamayya ta APC a Nigeria zasu ci gaba da ziyarar da suke yi ga wasu gwamnonin sabuwar PDP da suka balle daga jam'iyyar. Ranar Alhamis ne dai shugabannin jam'iyyar ta APC suka ziyarci gwamnonin Kano Rabi'u Musa kwankwaso da na Jigawa Sule Lamido A yau Juma'a kuma ake sa ran zasu je birnin Yolan jihar Adamawa don mika goron gayyatar shiga jam'iyyar ta APC ga gwamnan Jihar. Sai dai wasu daga cikin gwamnonin sabuwar PDP sun ce za su yi shawara tukunna. Gwamnan Kano Rabi'u Musa Kwankwaso ya bayyana cewa duk matakin da zai dauka, sai ya tuntubi jama'arsa tukuna. 'APC bata da akida da manufofi na hakika' Jami'yyar PDP mai mulki a Najeriya ta bayyana sabuwar gamayyar jam'iyyun adawar ta APC a zaman jam'iyyar munafukai wacce ba ta da akida da manufofi na hakika. A cikin wata sanarwa da ta aikewa kafafen watsa labarai, jam'iyyar ta PDP ta ce irin yadda APC take zawarcin wasu gwamnoninta, ya nuna karara cewar APC ba ta da jama'a da kuma 'yan takara da ka iya cin zabe, har sai ta shiga gandun PDP ta yiwo farauta. Sanarwar ta kara da cewa babu wani dan PDP na gaske da zai bar jam'iyyar ya koma APC.

Akalla mutane 7 sun mutu sakamakon fadan da aka fafata da ‘yan Bindiga a Najeriya

Rahotanni daga jihar Kano da ke yankin Arewa maso yammacin tarayyar Najeriya na nuna cewar an yi dauki-ba-dadi tsakanin Soji da wasu ‘yan Bindiga da aka zarga da kokarin kai harin kunar bakin Wake a Kano da Abuja. ‘Yan Bindigar dai sun bayyanawa Kamfanin dillancin labarai na AFP cewar akalla Soji Biyu 2 da wasu ‘yan Bindigar Biyar 5 sun mutu a wannan fafatawa da aka yi. Mai magana da Yawun Sojin Najeriya a yankin Captain Iweha Ikedichi, ya bayyana cwar bayannan sirrin da suka samu sun nuna masu cewar ‘yan Bindigar na kokarin kammala shirin kaddamar da wani harin ne a Abuja da Kano kuma Sojin sun gano jibgin Makamai a wannan harin da suka kai.

An sace mahaifiyar Ministan kudin Nigeriya

Wasu Yan bindiga sun sace mahaifiyar Ministan kudin Nigeriya, Ngozi Okonjo-Iweala, a garin su dake Ogwashi uku, a Jihar Delta. Bayanai sun ce, wasu mutane 10 ne suka sace mahaifiyar Ministan mai shekaru 82 ne a fadar Sarkin garin, Prof Chukwuka Okonjo da misalin karfi daya da rabi na rana. Mai magana da yawun Yan Sandan Jihar Delta, DCP Charles Muka, ya tabbatar da labarin, kuma ya zuwa yanzu dai, babu wanda ya dauki alhakin sace gyatumar.

Jam’iyyar APC ta fara zawarcin gwamnonin PDP guda Bakwai

Shugabannin Jam’iyyar adawa ta APC a Najeriya sun kai ziyara garin Kano da Jahar Jigawa da Sokoto inda suka gana da Gwamnonin Jahohin uku Rabi’u Musa Kwankwaso da Sule Lamido da Aliyu Wamakko domin zawarcinsu, a wani yanayi da kan iya zama baraka ga Jam’iyyar PDP mai mulki. An kwashe sa’o’I shugabannin na APC suna ganawa da gwamnonin Kano da Jigawa bayan sun gana da Gwamnan Sokoto Aliyu Magatakarda Wamakko a Sokoto bayan kammala biki bude Sabuwar Jami'ar Jahar. Shugabannin Jam’iyyar da suka gana da gwamnnonin sun hada da Janar Muhammadu Buhari tsohon shugaban kasa da Tsohon Gwamnan Lagos Bola Ahmad Tinubu da shugaban Jam’iyyar APC Bisi Akande da mataimakinsa Aminu Masari da kuma Nuhu Ribadu tsohon shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC. “APC ta shirya, ta zo ta ga da gwamnoni domin ta yi masu bayani game da tafiyarmu” Inji Buhari a lokacin da ya ke zantawa da Isa Dandago Wakilin RFI Hausa a Kano. Jam’iyyar APC ta samu kafar zawarcin Gwamnonin ne na PDP saboda takun sakar da suke yi tsakaninsu da uwar Jam’iyyarsu mai mulki a Najeriya Gwamnonin Sokoto da Kano da jigawa dukkaninsu gwamnoni da ke adawa da Uwar Jam’iyyar PDP, lamarin da ya sa suka kafa sabuwar PDP tare da jagorancin Alhaji Atiku Abubakar tsohon Mataimakin shugaban kasa. Sauran Gwamnonin da ke adawa da Uwar Jam’iyyarsu ta PDP sun hada da Gwamnan Niger Babangida Aliyu da Gwamnan Adamawa Murtala Nyako da Abdulfatah Ahmad na Kwara da kuma Gwamnan Rivers Rotimi Amaechi wadanda suka nemi a tsige shugaban PDP Bamanga Tukur. Mista Buhari yace sun gana da Wamakko na Sokoto da Kwankwaso na Kano da Lamido na Jigawa kuma sun yada wa gwamnonin manufofinsu. Tuni dai Jam’iyyar ta APC ta nada Gwamnan Lagos a matsayin wanda zai jagoranci tattaunawar zawarcin Gwamnonin na PDP. Sai dai Gwamnan Jigawa Sule Lamido ya kaucewa batun cewa ana neman zawarcinsa, yana mai cewa ya gana da shugabannin Jam’iyyar APC ne domin samar wa ‘Yan Najeriya hanyoyin ci gaba. Yanzu haka wata Majiya tace Shugabannin APC za su nufi zuwa Jahar Adamawa domin ganawa da Murtala Nyako babban mai adawa da jagorancin Bamanga Tukur na PDP.

An kori ministar sadarwar Ghana

An kori Ministar sadarwar kasar Ghana, Victoria Hammah bayanda aka dauki muryarta tana cewar za ta ci gaba da siyasa har sai ta mallaki dala miliyan daya. A muryarta da aka rarraba a Ghana ta ce " idan mutum nada kudi, zai iya juya mutane". Kawo yanzu Ms Hammah bata maida martani ba a kan wannan sakon ko kuma korarta da aka yi. Wakilin BBC a Accra ya ce ta taka muhimmiyar rawa wajen sake zaben Shugaba John Mahama a bara. A watan Agusta, ta ce tana fuskantar matsin lamba a kan ta saci kudin gwamnati saboda mutane sun zaci tana da arziki.

An kama 'Yan Najeriya masu safarar mata a Spain

'Yan sandan kasar Spain sun kama wasu 'yan Nijeriya su ashirin da biyar, wadanda suka ce suna fataucin mata daga Nijeriyar, suna tilasta masu aikin karuwanci a kasar ta Spain ko a wasu kasashen Turai. A wani bangare na aikin samamen , 'yan sandan sun kwace motoci casa'in da hudu a Madrid, da wasu karin ashirin da shidda a tashar jiragen ruwa ta Valencia. Bisa dukkan alamu gungun mutanen na shakare manyan motocin da giya ne, da kuma akwatunan talabijin, amma sai su like motocin domin boye kayan dake ciki. 'Yan sanda sun gano kayayyakin da aka boye na kimanin euro miliyan biyar cikin motocin. Ana kuma zargin gungun mutanen da aikata zamba da intanet, ta hanyar amfani da katunan bankin da suka sata.

Ra'ayi Riga: kara wa'adin dokar ta-baci

A jiya ne Majalisar dattawan Nijeriya ta amince da bukatar da shugaban kasar, Goodluck Jonathan, ya mika mata, na kara wa'adin dokar ta bacin da ya sanya a jihohin Borno, da Yobe da Adamawa. A ranar laraba ne dai shugaban kasar ya mika wannan bukata a bisa dalilan da ya ce matsalar hare-haren 'yan kungiyar Boko Haram ke ci gaba da kaiwa a wasu sassan jihohin, da ke haddasa asarar rayukan jama'a da dama. Sai dai yayin da wasu ke cewa daga lokacin da aka kafa dokar-ta-bacin an samu ci gaba a yunkurin karya lagon 'yan kungiyarta Boko Haram , akwai kuma masu ganin cewa al'amurra ma sun kara tabarbarewa ne.