labarun siyasa
Monday, 18 November 2013
Matsalar Tsaro a Najeriya
A shekarar 2009 ne Kungiyar Jama'atu Ahlil sunnah Lid Da'awati wal Jihad da ake kira Boko Haram ta kaddamar da hare hare domin daukar fansan kisan da aka yi wa Shugabansu Muhammad Yusuf da mambobinsu, kuma tun a lokacin Najeriya ta fada cikin matsalar tsaro bayan gwamnatin Yar'adua ta yi wa tsagerun Niger Delta afuwa. Kungiyoyin kare Hakkin bil'adama sun ce sama da mutane 3,000 ne suka mutu tun fara kaddamar da hare haren kungiyar Boko Haram, tare da zargin Jami'an tsaro da kisan fararen hula da sunan farautar 'yan kungiyar.
APC ta nemi a soke zaben Anambra
Jam'iyyar adawa ta APC a Nigeria ta bukaci hukumar zabe ta kasar, ta soke zaben gwamnan jihar Anambra wanda aka gudanar ranar Asabar da kuma wanda aka karasa ranar Lahadi.
Jam'iyyar ta yi zargin cewa kundin rajistar da aka yi amfani da shi a zaben gurbatacce ne.
Ta kuma ce a sakamakon haka an hana dubban magoya bayanta kada kuria'a .
Jam'iyyar ta APC ta kuma ce ta na da kwakkwarar shaida a kan lamarin.
Sai dai hukumar zabe mai zaman kanta ta musanta wannan zargi.
Ta kuma ce ba ta da dalilin soke zaben saboda sahihancin kundin rajistar da aka yi amfani da shi.
Za'a sake zabe a wasu sassan Anambra
Hukumar zabe ta kasa a Nigeria ta ce za ta sake gudanar da zaben gwamna a wasu sassa na jihar Anambra saboda matsalolin da aka fuskanta wurin gudanar da zaben.
Hukumar dai ta ce kawo yanzu jami'yyar APGA mai mulkin jihar ce kan gaba da kuri'u 174,710, jam'iyyar PDP mai mulkin Nigeria na biye da kuri'u 94,956 yayinda babbar jam'iyyar adawa ta APC ke da kuri'u 92,300.
Sai dai hukumar ta ce ba za ta iya baiyana wanda ya yi nasara ba sai bayan kammala ragowar zaben saboda kuri'un da suka rage ba'a kada ba sun dara tazarar da ke tsakanin jam'iyyar da ta zo ta daya da kuma mai bin ta.
Hukumar dai ta bayyana sakamakon zaben ne a daidai lokacin da 'yan takarar wasu jam'iyyu da suka hada da APC da Labour da PDP suka yi wani taron manema labarai a jiya, inda suka nuna rashin amincewarsu da zaben.
Wasu kungiyoyi masu zaman kansu ma dake sa ido a zaben, sun nuna rashin gamsuwarsu da yadda aka gudanar da shi.
Rahotanni sun ce ba'a kai kayan zabe da wuri ba a wasu mazabu, kuma a rajistar masu zaben ma babu sunayen mutane da dama, kazalika ma suka ce akwai wasu wuraren da ba a yi zaben ba.
Bafaranshen da aka kama a Nigeria ya isa gida
Bafaranshen nan da aka sace a Nigeria ya isa gida bayanda ya tsere daga wadanda suka yi garkuwa da shi a wani yanayi da shugaban kasar Faransa Francois Hollande ya ce yayi kama da littattafan labarai.
Thursday, 14 November 2013
An sace shanu sama da 1000 a Pilato
Sakataren kudi na kungiyar Miyatti Allah ta Fulani makiyaya reshen jihar Pilato Malam Salihu Jauro ya ce lamarin ya faru ne a kauyen Sit dake tsakanin Pankshin da Langtan ta arewa.
Makiyayan na neman mahukunta da su basu cikakken tsaro tare da dabbobinsu.
A mafi yawan lokuta dai satar shanu na haddasa rikicin kabilanci a yankin.
Jihar Pilato ta sha fama da rikicin kabilanci da addini tsawon shekaru 14.
Najeriya na neman sulhu da Boko Haram
Gwamnatin Najeriya ta ce abin da ta sa a gaba shi ne kokarin sulhuntawa da 'yan kungiyar da wasu ke kira Boko Haram ba maganar gurfanar da su gaban kuliya ba.
Mahukunta a Najeriyar sun ce ba a maganar shari'a sai sulhu ya gagara.
Gwamnatin dai na mai da martani ne dangane da matakin da majalisar dinkin duniya ta dauka na sanya 'yan kungiyar Jama'atu Ahlis sunnah lidda'awati wal jihad da wasu ke kira Boko Haram a sahun masu aikata laifukan yaki idan aka tabbatar da aikata laifukan da ake zarginta da yi.
Wannan matakin zai ba da kafar gurfanar da duk wani dan kungiyar da ake zargi a kotun hukunta laifukan yaki ta duniya da ke Hague.
Boko Haram: Mutane 40,000 sun gudu Niger
Mutane kusan dubu 40 ne suka tsallaka iyakar Nigeria zuwa Jamhuriyar Niger sakamakon rikicin kungiyar Boko Haram.
Subscribe to:
Comments (Atom)